Gce All School News Education Guides Technology General

JOIN OUR WAEC & NECO WHATSAPP SAPP GROUP

Waec 2022 Hausa Language Objective And Theory Questions And Answers
By on May 31st, 2022. Waec
0

HAUSA OBJ
1-10: DCBACDACBD
11-20: ADCBCAAACB
21-30: BBCCCDABCA
31-40: DACDBBBBAB
41-50: DCDCADADCC
51-60: CCCDABDCBD

HAUSA-ESSAY ANSWERS ANSWERS
(1)
KUDA WAJEN KWADAYI AKAN MUTU
An yi wani mutum da ya shahara wajen neman mata, don kuwa abokansa har wani kirari suke ma sa wai “kuda ba ka haram”. Ba komai ya sa suke ma sa wannan kirari ba illa duk inda ya ga mace sai ya takale ta da zancen banza.
Ganin yadda al’amarin abokinsu ya ta’azzara wadanda za su iya daga cikin abokansa, suka dauki gabarin ba shi shawara kan ya guji neman mata saboda illolin dake tattare da aikata hakan, saboda tarin zunubi da a kullum yake kwasa, kuma ga shi ba’a sanar da bawa lokacin mutuwarsa balle ya tuba kafin lokacin, baya ga cututtuka da ake dauka sakamakon wannan mummunan aiki, amma duk da haka ya yi kunnen uwar shegu da su.
Wata rana ya shiga wani wajen sayar da abinci don ya cika cikinsa, zamansa ke da wuya, sai wata mace ta shigo don ta sayi abinci, akai dace ta zauna kusa da shi, kowannen su ya fadi abincin da yake bukata aka kawo ma sa.
Bayan sun kammala cin abincin sai ya dauko kudi ya ce, a dauki na sa da kuma na wannan mata, ko da ta ji haka, sai ta ce, a’a ya kyale shi za ta biya, sannan ta yi ma sa godiya. Amma duk da haka gogan naka ya nace shi sai ya biya kudin, daga karshe da ta ga ba yadda ta iya sai ta hakura ya biya.
Ta nufi kofar fita, ya biyo ta ya ce, ta zo ya kai ta inda za ta je,a motarsa, sai ta shaida ma sa cewa a motarta ta zo, sai ya ce, to tunda kin ki shiga tawa motar, ke rage min hanya a motarki, sai ta ce ya shiga.
Shigarsa motar ke da wuya, ta tayar da ita suka runtuma, ba ta tsaya a ko ina ba, sai wani barikin sojoji dake garin. Isar su bakin kofar shiga, ya ga an bude ma ta kofa da sauri, ta na zuwa kofar wani gida ta yi fakin da motar ta shiga gida. Ashe matar wani babban soja ce a wannan bariki.
Ta na shiga gida akai sa’a mijin na ciki, sai ta ba shi labarin yadda su ka yi da wannan manemin mata. A nan fa soja ya fito, ya umarci wasu kuratan soja kan su kawo shi gabansa ya na falo a zaune.
Ko da ya shigo falo jikinsa na rawa, sai mijin matar ya tambaye shi, “Me ne ne hadinka da mata ta ? Saboda tsabar kyarmar jiki ya gagara ba shi amsa. Can fa soja ya tafasa ransa ya baci, ya daka ma sa tsawa ya ce, “To me ya kawo ka gidana ?. Sai kawai ya ce karar kwana !.
Ko da sojan ya ji haka sai ya bushe da dariya, ya ce, da kuratan sojan su raka shi kofa. To sai dai hausawa na cewa, “Ba’a bari a kwashe dai-dai”, sojojin nan su ka ce, ba za su yi rakiyar banza ba, sai da suka ba shi na jaki sannan su ka iza keyarsa su ka ce, nan gaba ma ya kara.
Ai kuwa tun daga wannan rana ko abokansa sun ce “Kuda ba ka haram” sai ya ce da ke nan.

Join Our Whatsapp Group

About Author
Jambclass

I’m a blogger living in Nigeria. I like to share education guides and information from various sources. I created Jambclass to serve as a platform to disseminate quality, credible and dependable information regarding various ways to excel academically. I strive to keep Nigerian youths and students informed. I started this Blog with the Vision To Inspire and Empower Young Persons; helping them Realize and Maximize their Potential.

RECOMMENDED TOPICS
No Comments Yet

Leave a Reply

NOTE:- Your comment will appear after it has been approved by an admin.